Zakariya 1:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka ce musu, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku juya daga mugayen hanyoyinku da mugayen abubuwan da kuke yi.’ Amma ba su saurara ba, ko ma su kula da ni, in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.