Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.
“Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!
zai kuwa kasance a wuri mai tsarki; amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe dutse kuma da zai sa su fāɗi. Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama tarko da raga.
Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.