16 Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.
16 Ya Ubangiji, ka sa kunya ta rufe su, Don su so su bauta maka.
Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.
Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”
Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi.
Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.
Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.