“Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Tabbatacce mugunta tana ƙuna kamar wuta; tana cin ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya, ta sa wuta a jeji mai itatuwa masu yawa, don yă yi murtuke hayaƙi har zuwa sama.
An riga an shirya wurin ƙonawa; an shirya shi saboda sarki. An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi, da isashen wuta da itacen wuta; numfashin Ubangiji, yana kamar kibiritu mai ƙuna, da aka sa masa wuta.
Ko da yake mutane suna ruri kamar sukuwar raƙuman ruwa, sa’ad da ya tsawata musu za su gudu can da nisa, aka kore su kamar yayinda iska ya hura a kan tuddai, kamar tattake kuma a cikin guguwa.