Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”
“A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, tuddai kuma za su malmalo madara; dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.
“An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.
“Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama; bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci. Bari ƙasa ta buɗe, bari ceto ya tsiro, bari adalci ya yi girma tare da shi; ni, Ubangijine, na sa ya faru.
A maimakon tagulla zan kawo zinariya, azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe. A maimakon katako zan kawo tagulla, baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu. Zan sa salama ta zama gwamnarki adalci kuma mai mulkinki.