Gama a cikin Nassi an ce, “Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona, zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja, wanda kuma ya dogara gare shi ba zai taɓa kunyata ba.”
Bari masu tsananta mini su sha kunya, amma ka kiyaye ni daga shan kunya; bari su tsorata, amma ka kiyaye ni da razana. Ka kawo musu ranar masifa; ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.
Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi.
Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”