5 Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
5 Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah, Ka san irin wawancin da na yi!
Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
Idanuna suna a kan dukan hanyoyinsu; ba a ɓoye suke daga gare ni, kuma zunubansu ba a ɓoye suke a idanuna ba.
Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi.
Wane ne zai iya rabe kurakuransa? Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.
Ko ka duba zuciyata, ka kuma bincike ni da dare, ko ka gwada ni, ba za ka sami kome ba; na yanke shawara cewa bakina ba zai yi zunubi ba.
Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina.