Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.
Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai ’ya’yansu kuma a cikin mutane. Dukan waɗanda suka gan su za su san cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”
Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’