Amma maganata da dokokina da na umarta ta wurin bayina annabawa fa, ashe, ba su tabbata ba a kan kakanninku? “Sa’an nan suka tuba suka ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki ya yi mana daidai abin da hanyoyinmu suka cancanci mu samu, kamar dai yadda ya yi niyya yi.’ ”
A wannan rana zan yi fushi da su, in kuma yashe su; zan ɓoye fuskata daga gare su, za a kuwa hallaka su. Masifu masu yawa da wahaloli masu yawa za su auka musu, a wannan rana kuwa za su ce, ‘Masifun nan sun same mu domin Allahnmu ba ya tare da mu’