Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Zabura 66:6 - Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

6 Ya sa teku ta zama busasshiyar ƙasa, Kakanninmu suka haye kogi da ƙafa. A can muka yi farin ciki saboda abin da ya yi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Zabura 66:6
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko.


Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.


Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba.


Amma Isra’ilawa suka wuce cikin teku a busasshiyar ƙasa, ruwa kuwa ya yi musu katanga dama da hagu.


Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.


Ku ce musu, ‘Isra’ilawa sun ƙetare kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ