Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah.
Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.