2 Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a.
2 Ya Sarkina, Allahna, Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.
Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo.
Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela
Gama Ubangiji ne alƙalinmu, Ubangiji ne mai ba mu dokoki, Ubangiji ne sarkinmu; shi ne wanda zai cece mu.
Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.
Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.
Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya.
Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.
Ubangiji Sarkin har abada abadin ne; al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa.
Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana.
Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”