Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.
Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.