Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.
ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi.
Dukan garkunan Kedar za su taru a wurinki ragunan Nebayiwot za su yi miki hidima; za a karɓe su kamar hadayu a kan bagadenki, zan kuma darjanta haikalina mai ɗaukaka.
Dawuda ya gina bagade wa Ubangiji a can ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wuta daga sama a kan bagaden hadaya ta ƙonawa.
Sai wuta ta fito daga gaban Ubangiji ta cinye hadaya ta ƙonawa da sassan kitsen a kan bagaden. Sa’ad da dukan mutane suka ga haka, sai suka yi ihu suna farin ciki, suka fāɗi rubda ciki, suka yi sujada.