Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan; ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi. Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu, ku jeji da dukan itatuwanku, gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub, ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu; bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki. Bari mutanen Sela su rera don farin ciki; bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.