3 Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.
3 Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji, Daga yanzu har abada!
Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.
mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji.
Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.