1 Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji.
1 Yabo Ya tabbata ga Ubangiji! Ku bayin Ubangiji, Ku yabi sunansa!
Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji; ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.
Yabi Ubangiji. Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji, wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.
’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.
Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!”