Yunana 2:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 “Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka marasa amfani Sun daina yi maka biyayya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.