Za su zauna a ƙasar da na ba wa bawana Yaƙub, ƙasar da kakanninsu suka zauna. Su da ’ya’yansu da ’ya’ya ’ya’yansu za su zauna a can har abada, kuma Dawuda bawana zai zama sarkinsu har abada.
Ku duba Sihiyona, birnin shagulgulanmu; idanunku za su ga Urushalima, mazauni mai lafiya, tentin da ba za a taɓa gusar ba; wanda ba a taɓa tumɓuke turakunsa ba, ko a tsinke igiyoyinta.