4 Suna da kamannin dawakai; suna gudu kamar dokin yaƙi.
4 Kamar doki take, Tana gudu kamar dokin yaƙi.
Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane.
Sa’an nan kofatan dawakai suka ƙwaƙula, suna sukuwa, haka dawakansa masu ƙarfi suke tafiya.
Ku ji karar bulala da kwaramniyar ƙafafu, da sukuwar dawakai da girgizar kekunan yaƙi!