Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko ’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha.
A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.
Zan sa Ruhuna a cikinku za ku kuwa rayu, zan kuma zaunar da ku a ƙasarku. Sa’an nan za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata, in ji Ubangiji.’ ”
“Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari.