Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yowel 2:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 “Zan kori sojojin arewa nesa da ku, in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma, kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum. Warinsu kuma zai bazu; ɗoyinsu zai tashi.” Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 Zan kawar muku da waɗanda suka zo daga arewa, Zan kori waɗansunsu zuwa cikin hamada. Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikin Tekun Gishiri, Zan kori sahunsu na baya, zuwa cikin Bahar Rum. Gawawwakinsu za su yi ɗoyi. Zan yi musu haka saboda dukan abin da suka yi muku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yowel 2:20
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.


“Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.


Za a jefar da waɗanda aka kashe gawawwakinsu za su yi wari; duwatsu za su jiƙu da jininsu.


Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum.


A wajen gabas iyakar za tă kama tsakanin Hauran da Damaskus, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra’ila, zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.


Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar.


Hazayel ya ce, “Yaya bawanka, wanda yake kare kawai, zai iya aikata wannan irin abu?” Elisha ya ce, “Ubangiji ya nuna mini cewa za ka zama sarkin Aram.”


Aka jibga su tsibi-tsibi, ƙasar ta yi ɗoyi saboda su.


Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.


Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ