30 Yoshuwa kuwa ya yi wa Ubangiji, Allah na Isra’ila bagade a Dutsen Ebal,
30 Joshuwa ya gina wa Ubangiji Allah na Isra'ilawa bagade a bisa Dutsen Ebal.
“ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka.
Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden.
Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku kakkafa waɗansu manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.