Yoshuwa 8:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 Ya rataye sarkin Ai a kan itace, ya bar shi a can har yamma. Da rana ta fāɗi, Yoshuwa ya umarta a ɗauke gawar sarkin a jefa a gaban ƙofar birnin. Suka kuma tara manyan duwatsu a kan gawar, tsibin na nan har wa yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki29 Ya rataye Sarkin Ai a bisa itace har maraice. Sa'ad da rana take faɗuwa Joshuwa ya umarta su ɗauke gawarsa daga itacen, su jefa a ƙofar birnin, su tsiba duwatsu da yawa a kanta. Tsibin duwatsun yana nan har wa yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |