Yoshuwa kuma ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, me ya sa ka sa mutanen nan suka ƙetare Urdun don ka bari mu shiga hannun Amoriyawa su hallaka mu? Kila da mun haƙura mun zauna a ɗaya gefen Urdun da ya fi mana!
Lokacin da mayaƙan suka komo sansani, dattawan Isra’ilawa suka yi tambaya suka ce, “Me ya sa Ubangiji ya sa muka sha ɗibga a hannun Filistiyawa? Bari mu kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Shilo. Domin yă tafi tare da mu yă ba mu nasara kan abokan gābanmu.”