Yoshuwa 5:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Sai ya sa yaransu ne suka taso a maimakonsu, su ne waɗanda Yoshuwa ya yi wa kaciya. Sun kasance ba kaciya gama ba a yi musu ba a hanya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 'Ya'yansu ne kuwa waɗanda Ubangiji ya tā da su a maimakonsu, su ne Joshuwa ya yi wa kaciya, gama ba su da kaciya, domin a hanya ba a yi musu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.