Yoshuwa 5:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 To, da dukan sarakunan Amoriyawa na yammancin Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawan da suke bakin teku suka ji yadda Ubangiji ya busar da kogin Urdun a gaban Isra’ilawa, har sai da dukansu suka ƙetare, zuciyarsu ta narke, suka karaya sosai har ma suka rasa samun ƙarfin hali su fuskanci Isra’ilawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.