Yoshuwa 22:25 - Sabon Rai Don Kowa 202025 Ubangiji ya sa Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku, ku mutanen Ruben da mutanen Gad! Ba ku da rabo cikin Ubangiji.’ ’Ya’yanku za su iya sa ’ya’yanmu su daina tsoron Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki25 Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra'ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ To, da haka 'ya'yanku su hana 'ya'yanmu yi wa Ubangiji sujada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’