ya sauka zuwa yammancin bakin iyakar Yalfetiyawa har zuwa yankin Bet-Horon wanda yake cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, ya gangara ya yi ƙarshe a Bahar Rum.
Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda.