Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 17:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

4 Suka zo wurin Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun, da shugabannin, suka ce, “Ubangiji ya umarci Musa ya ba mu gādo tare da 'yan'uwanmu maza.” Sai ya ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu bisa ga umarnin Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 17:4
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu.


Ga wuraren da Isra’ilawa suka sami gādo a ƙasar Kan’ana waɗanda Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin iyalai kabila-kabila na Isra’ila suka raba musu.


Dalilin ke nan Manasse ya sami kashi goma ban da ƙasar Gileyad da Bashan a gabashin Urdun,


’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.


Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.”


Saboda haka ’ya’yan Zelofehad mata suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.


To, a lokacin, sai shugabannin iyalan Lawiyawa suka je wurin Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin sauran iyalan kabilu na Isra’ila a


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ