Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.
Sa’ad da suke a kwari kusa da Bet-Feyor, gabas da Urdun, a ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, da Musa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi sa’ad da suka fito daga Masar.
dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.