Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 11:14 - Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Isra’ilawa suka kwashi ganima da dabbobi na waɗannan birane, amma suka karkashe mutanen duka da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

14 Isra'ilawa kuma suka kwashe ganima ta abubuwa masu tamani na biranen game da shanu, amma suka kashe kowane mutum da takobi, har suka hallakar da su, ba su bar kowa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 11:14
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka karkashe duk mazaunan ƙasar da takobi, ba su bar wani mai numfashi ba, suka kuma ƙona Hazor.


Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta.


Amma Isra’ilawa suka kwashe ganima da dabbobin birnin nan yadda Ubangiji ya umarci Yoshuwa.


Game da mata, yara, dabbobi da kuma sauran abubuwan da suke cikin birnin, za ku iya kwasa waɗannan a matsayin ganima wa kanku. Za ku kuma yi amfani da ganimar da Ubangiji Allahnku ya ba ku daga abokan gābanku.


Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima.


Amma fa, a cikin biranen al’ummai da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, kada ku bar wani abu mai numfashi da rai.


Duk da haka Isra’ilawa ba su ƙone biranen da suke kan tuddai ba, sai Hazor kaɗai Yoshuwa ya ƙone.


Yadda Ubangiji ya umarci bawansa Musa, haka Musa ya umarci Yoshuwa, shi kuwa ya yi duk abin da Ubangiji ya umarci Musa.


Za ku yi wa Ai yadda kuka yi wa Yeriko da sarkinta, sai dai za ku kwashe ganima da dabbobinta su zama naku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”


Sa’ad da Yehoshafat da jama’arsa suka je kwasar ganima, sai suka sami shanu masu yawan gaske, da kayayyaki, da tufafi, da abubuwa masu daraja, waɗanda suka yi ta kwasa har suka gaji. Kwana uku suka yi suna kwasar ganimar saboda yawanta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ