Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yoshuwa 10:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

11 Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yoshuwa 10:11
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi. Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna, kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa, zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.


Daga sama taurari suka yi faɗa, daga bakin tekuna suka yi yaƙi da Sisera.


Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.


Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.


saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke.


Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.


A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu.


Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama.


“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara


Gama Ubangiji Allahnku, yana tafe tare da ku, zai yaƙi abokan gābanku dominku, yă ba ku nasara.”


Yaƙin ya bazu a duk fāɗin ƙauyukan, abin da kurmin ya ci kawai a ranar ya fi yawan abin da aka kashe da takobi.


waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa?


Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?


Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim, zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyon don yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba, yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ