Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
“Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’ ”