Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba.
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”
Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”