Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 2:15 - Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

15 Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 2:15
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.


Da Yesu ya ce, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.


Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.


Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.


A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi.


Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”


Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ