Sa’ad da lokaci ya yi kusa a yi Bikin Ƙetarewa na Yahudawa, da yawa suka haura daga ƙauyuka zuwa Urushalima, don su tsarkake kansu kafin Bikin Ƙetarewa.
Sau uku a shekara dukan maza su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da ya zaɓa; a Bikin Burodi Marar Yisti, da a Bikin Makoni, da kuma a Bikin Tabanakul. Babu wani da zai bayyana a gaban Ubangiji hannu wofi.
Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,
Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.