Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.
Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”
An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi
“An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali.