Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; na tattara mur nawa da kayan yajina. Na sha zumana da kuma kakinsa na sha ruwan inabina da kuma madarana. Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu.
Suka shiga suka mallake ta, amma ba su yi maka biyayya ba, ba su kuma bi dokarka ba; ba su yi abin da ka umarce su ba. Saboda haka ka kawo masifa a kansu.
Sai na yi kamar yadda aka umarce ni. Da rana na fitar da kayana da na tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma na huda katanga da hannuwana. Na kwashe kayana da dare, na ɗauke su a kafaɗuna yayinda suke kallo.