Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 13:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 13:20
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”


Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”


“Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”


“Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’


Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.


To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa,


Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ