Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni; jiragen Tarshish kuma su ne a gaba, suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa, tare da azurfa da zinariya, domin su girmama Ubangiji Allahnki, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya cika ki da daraja.
Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba, kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku, saboda Ubangiji Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya darjanta ku.”
Da fari almajiransa ba su gane dukan wannan ba. Sai bayan da aka ɗaukaka Yesu, sa’an nan suka gane cewa an rubuta waɗannan abubuwa game da shi ne, har ma suka yi masa waɗannan abubuwa.
Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi.
Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.