Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku kafin ya kawo duhu, kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe a kan tuddai masu duhu. Za ku sa zuciya ganin haske amma zai mai da shi duhu mai kauri ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.
Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi; saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba. Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya; ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba.