Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’?
“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.
Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.
Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.