Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.
Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.