Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.
Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba.
“Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi?
ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’