Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”
Sai Yesu ya ce musu, “Haske zai kasance da ku na ɗan lokaci. Ku yi tafiya yayinda hasken yana nan tare da ku, kada duhu yă cim muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda za shi ba.
Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba.
Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu.
Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai.