Yahuda 1:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Amma lokacin da babban mala'ika, Mika'ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika'ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”