W.Yah 9:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki21 ba su kuma tuba da kashe-kashenkai da suka yi ba, ko sihirinsu, ko fasikancinsu, ko kuma sace-sacensu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.