Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.
Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in fitar da kai tare da dukan sojojinka, dawakanka, mahayan dawakanka saye da makamai, da kuma jama’a mai girma masu riƙe da garkuwoyi manya da ƙanana, dukansu da takuba a zāre.
Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan.
“A lokaci ƙarshe sarkin Kudu zai tasar masa da yaƙi, sarkin Arewa kuwa zai tunzura, yă tasar masa da kekunan yaƙi da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, yă ci su da yaƙi, yă wuce.