Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 8:13 - Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

13 Sa'an nan da na duba, na ji wani juhurma mai jewa a tsakiyar sararin sama, yana kuka da ƙarfi, yana cewa, “Kaito! Kaito! Kaitonku, ku mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala'ikun nan uku suke shirin busawa!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 8:13
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba.


Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.


Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a.


wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.


Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah,


Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis.


Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?


Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.


Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya.


Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.


Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai.


Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ